tgindex
Abdurrahman Muhd Sani Umar

Abdurrahman Muhd Sani Umar

Статистика
Последний пост
14 авг.
Последнее чтение
13 авг.
Постов за неделю
3
Всего постов
28
Тип
открытый
Язык
und
В каталоге с
13 авг.
Подписчики
3 526
−2 за 3 дн.
Сутки
0
0,00%
Неделя
 
Месяц
 
Просмотров на пост
491
28 постов
Вовлечённость
13,9%
к подписчикам
Постов в день
0,4
всего 28
Упоминаний
0
каналов
Охват размещения
оценка
1/24сутки в ленте
192
1/48двое суток
220
1/72трое суток
237

Оценка по просмотрам недавних постов: пост набирает почти всё за первые сутки.

Посты

  • без подписи

  • Maƙiya sun fi so da fifita gafalalle a kan kwaɗayayye, domin na biyun sai an yi dawainiya da shi, sannan kuma ba zai zage ya yi aikin da su ke so yadda ya kamata ba, yayin da na farkon zai yi aiki tuƙuru kuma a kyauta. Sannan ikhlasinsa da jajircewarsa za su sa mutane su rudu da shi. Shi ya sa yake da haɗari a samu ire-iren na farko a matakin shugabanci da jagoranci musamman a bangaren siyasa da addini, domin zai halakar ne a tsammaninsa kuma tseratarwa yake yi !!

  • *Karatun Littafin* *نبي الرحمة سيرة ودروس وعبر* Drs na 59 *Mal. Abdurrahman Muhd Sani Umar* Daga Masallacin Markazul Imamul- Bukhari Rijiyar Zaki Kano. 11/08/2026 - 29/02/1448 - Tsari da shiri da muhimmancinsa. - Darajar Abubakar (RA) da falalarsa Domin samun karatukan malam ku bibiyi waɗannan shafuka:* Whatsapp: (A) https://chat.whatsapp.com/EYip4EPotboLSTwqiPKkfv (B) https://chat.whatsapp.com/LvMW02BVKegCbubI7E3ZbS?mode=wwc Telegram: https://t.me/Abm_Sani Facebook: https://www.facebook.com/am.sani3?mibextid=ZbWKwL YouTube: https://youtube.com/@abdurrahmanmuhammadsani7823?si=SqgPVhLHWJTTBRIm

  • Gina masallatai, ciyar da mutane, yi wa iyaye hidima, kai mutane Hajji da Umara, da sauran ayyukan alheri, ba sa taɓa wanke dukiyar da aka samo ta hanyar zalunci da haram. Domin a wajen Allah, ba za a iya yin “Money Laundering” da dukiya kamar yadda ake yi a duniya ba. Wannan shi ne abin da azzaluman shugabanni, gurbatattun ’yan siyasa, mawaƙa, ’yan nanaye, da sauran duk masu samun dukiyar haram ya kamata su sani. Allah Tsarkakke ne, kuma ba Ya karɓar komai sai abin da yake tsarkakakke.

  • *Karatun Littafin* *الأربعون النووية* Drs na 61 *Mal. Abdurrahman Muhd Sani Umar* Daga Masallacin Imamu Musulim, Ɗanbare Unguwar katako, Kano 22/02/1448 06/08/2026 Hadisi na 19 * Darrussa dake cikin hadisin *Domin samun karatukan malam ku bibiyi waɗannan shafuka:* Whatsapp: (A) https://chat.whatsapp.com/EYip4EPotboLSTwqiPKkfv?mode=wwt (B) https://chat.whatsapp.com/LvMW02BVKegCbubI7E3ZbS?mode=wwc Telegram: https://t.me/Abm_Sani Facebook: https://www.facebook.com/am.sani3?mibextid=ZbWKwL YouTube: https://youtube.com/@abdurrahmanmuhammadsani7823?si=SqgPVhLHWJTTBRIm

  • Za ka taƙaita yaƙin da yake wakana tsakanin America da Iran da faɗin Bahaushe cewa: "Garin neman gira, an rasa ido." Domin yadda lamuran suke wakana a yankin Gabas ta Tsakiya, kama daga tarwatsewar ƙawancen Shi'anci da Iran take jagorata ta hanyar yi wa Hizbullahi raga-raga, rugujewar gwamnatin Asad a Syria, da kuma halin rauni da Iran ta shiga sakamakon kashe jiga-jiganta da kuma matsin tattalin arziki, banda saɓani na cikin gida tsakanin talakawan ƙasar da tsarin gwamnatin Wilatul Faqih, da saɓanin tsakanin jiga-jigan wannan tsari kan waye zai zamanto halifan Murshid. Duk waɗannan abubuwan, idan ka kalle su a lokacin, za ka iya cewa ƙiris ya rage tsarin mulkin Iran ya kai ƙasa, domin Gara ta yi nisa wajen cinye sandar da yake dogarawa da ita. Sai dai, shigar Isra'ila da America domin yaƙar Iran za ka iya cewa ya sake busa wa Iran ɗin rai, sakamakon abin da ya biyo baya. Kafin yaƙin, mashigin ruwa na Hormuz mashigin ruwa ne na duniya; bayan yaƙin kuma ya zama ƙarƙashin ikon Iran. Kafin yaƙin, America tana da sansanonin soja guda 19, waɗanda dukkansu suke aiki yadda ya kamata, kuma suna hana maƙiyan America da Isra'ila yin abin da suke so, tare da sanya razani. Bayan yaƙin, an lalata mafi yawansu, yayin da sauran suka zama ba su da cikakkiyar ƙwarewar gudanar da aikinsu. Kafin yaƙin, tsarin mulkin Iran yana da rauni, yana dab da rugujewa, kuma akwai saɓani kan wanda zai gaji Murshid. Bayan yaƙin, Iraniyawa sun dunƙule, tsarin mulkin ya ƙara ƙarfi, farin jininsa ya ƙaru, kuma an warware batun wanda zai gaji Murshid ta hanyar zaɓen wani sabon Murshid matashi mai zafin kai, wanda ke da ƙudurin ɗaukar fansa. Kafin yaƙin, Isra'ila ta shafe kusan shekara 20 tana yi wa Iran barazanar kai mata hari ta hanyar soja. Bayan yaƙin kuwa, Isra'ila ta daina yin irin wannan barazana, ta koma matsayin kariya, tana cewa: "Idan Iran ta kai mana hari, za mu mayar da martani." Yanzu matakan da suka rage wa America domin warware waɗannan sababbin matsaloli sune: na farko, kai hari mai kan uwa da wabi a kan abubuwan more rayuwar ƙasa, kama da gadajoji, tashoshin wutar lantarki, matatun tace ruwan sha, da sauransu. A kwanakin baya shi aka ɗauka, sai dai, duba da irin mummunar hasarar da zai janyo wa ƙasashen Gulf, waɗanda a kansu ramuwar za ta kasance, da kuma ƙarancin makaman kare sararin samaniya na America da take fama da shi, shi ya sa aka dakata zuwa wani lokaci. Mataki na biyu kuma, wanda shi ne mafi hatsari, kuma "Final Solution" na matsalar Iran, shi ne amfani da makamin kare dangi wanda ake kira "Tactical Nuclear Bomb", domin tirsasa wa ƙasar miƙa wuya, kwatankwacin yadda aka tursasa wa Japan miƙa wuya a 1945. Wadannan matakai biyu sune suka ragewa America, ko wannensu babu tabbas ya bada sakamakon da take fata saidai ma ya kara dagula yankin gaba daya.

  • без подписи

  • da rugujewarsu da kuma rugujewar tsarin da suka gina duniya akai. A ƙarshe yana da kyau masu da'awa su ƙara fahimtar da mutane sunnunonin Allah, hakanan su fahimtar da su ma'aunan cigaba da jin daɗin rayuwa, muna neman cigaba da ɗaukaka a duniya amma ba irin na America ko Ingila ko Russia ko China ko wata ƙasar da ba ta ka kan tsarin Allah ba, muna neman cigaba da ɗaukaka irin ta wayewar musulminci wayewar da ta ginu akan cikakken adalci da ƙin zalinci, ta ginu akan ruhi da gangar jiki, ta ginu akan raya duniya da kuma gina lahira.

  • 4 August 2024: Me yasa zunubai ba su hana turawa cigaba ba sai mu da muke musulmai ? Wannan tambayar tana yawan yawo a bakin wasu musulmai duba irin halin ake ciki na wuya da ƙunci da zaluncin shugabanni, ta kuma ƙara yawaita a kwanakinnan sakamakon kiraye-kirayen da wasu masu da'awa suke yi na koma wa ga Allah da kuma ishara ga cewa zunubai da ayyukan saɓo sune dalilan tsintar kanmu a cikin wannan halin, saidai hakan ba ya gamsar da gama garin mutun musamman idan ya ga cewa ga ƙasashen da nan ne maɓuɓɓugar zunubai da laifuka harma da kafirci da fito na fito da Allah amma su ne lamba ɗaya a duniya a duk wani ɓangaren na cigaba da jin daɗin rayuwa Rashin samun gamsasshiyar amsa game da wannan tambayar yana iya sanadiyar haifar da sakamako masu hatsari mafi ƙarancinsu shine haifar da tabo mai girma a zuciyar mutane game da addini. Amsar wannan tambayar a taƙaice ita ce: 1- Idan aka ce zunubai ba iya zunubai na ɗaiɗaiku ake nufi ba harma da na gama gari gaba ɗaya, ba su kuma taƙaita akan iya talakawa ba har dama shugabannin tsuke ma'anar kalmar zunubi da taƙaice ta shi ya haifar da wannan gurgurwar fahimta. Game bayani sosai akan wannan gaɓar duba wannan link ɗin. https://www.facebook.com/share/p/QSNEV65yvsWmYRog/?mibextid=oFDknk 2 - Komawa ga Allah ba ya nufin taƙaituwa akan iya addu'a da azimi da sadaka da wasu ibadu na ɗaiɗaikun mutane ba, hakanan ba kuma taƙaita a iya kan talakawa ba, cikakkiyar koma wa ga Allah ita ce da talakawan da shugabannin kowa ya sauke haƙƙi da nawin da Allah ya ɗora masa matuƙar aka samu ɗaya babu ɗaya to lalle za a samu tangarɗa. Bayani ya taɓa gabata akan wannan gaɓar filla-filla duba wannan link ɗin: https://www.facebook.com/share/p/DBS4Xm2N3qFin5E4/?mibextid=oFDknk 3- Shiga cikin ƙunci da tsananin rayuwa ba ya nufin cewa lalle zunubai ne musabbin haka, domin Allah kan sanya mumuni a wanni yanayi mara daɗi domin jarraba shi, da kuma kankare masa zunubai da ma ɗaukaka matsayarsa da sauran hikimomi, a kuma gefe guda kuma yakan buɗa wa kafirai duniya domin yi musu talala, shi yasa za ka gaa tarihi Annabawa da salihan bayi sun sha wahala a daidai lokacin da za ka ga kafiran lokacin su suna cikin daula da ni'ima da jin daɗi, waɗannan misalai biyu su ake kira da "Sunnar ibtila'i" da kuma "Sunna talala", ta farkon ta keɓanta ga mumunai ne kawai ta biyun kuma ta kafirai ce waɗanda suka kangarewa Allah, fahimtar sunnunonin Allah da kashe-kashensu zai ƙara fito da wannan batun. 4- Yana da kyau a fara sanin menenema cigaban da kuma jin daɗin da ake tinanin turawa suna cikinsa, idan cigaba na gine-gine da ƙere-ƙere shi ake nufi, wannan tabbas suna da shi wannan kuma yana koma wane zuwa ga sunnar Allah ta taimakon wanda ya kama sababi ba tare da la'akari da waye shi ba, idan kuma ana nufin ci gaba na jin daɗin rayuwa ne to wanda yake faɗan hakan bai san irin ƙazantacciyar rayuwar da turawan suke ba wanda hakan ya haifar musu matsaloli da yawa kama da damuwa da rashin nutsuwa da kwanciyar hankali, da rashin sanin wai me maƙasudin rayuwar, irin wannan shi ya haifar musu da yawan cutukan damuwa da kuma yawan kashe kai, banda ɗumbin laifuka na kisa da sata da fashi fa fyaɗe har takai ana lissafa aukuwar laifuka da adadin mintina da awanni, ya zamanto yadda ake lissafa su a gaba gaba wajen cigaban gine gine-gine da ƙere-ƙere haka ake lissafa su a gaba gaba wajen aikata munan laifuka da yawan cutukan damuwa da kashe kai !! Wannan kuma ita ce sunnar Allah ga wanda ya kaucewa shiriya ba zai taɓa samun jin daɗi na zuciya da ruhi ba ko da ya samu na gangar jiki da na zahiri wannan kuma ita ce mafi tsanani da girma uƙuba !!. A taƙaice za mu iya cewa ƙasashen da ake leƙe ake zaton aljanna ce, to aljannar Dujal ce !! 5- Da yawa mutane ba su sani ba halin da ake ciki ɗinnan turawan da ake leƙe ana ganin sun cigaba sune musabbabin halin da muke ciki, hasalima cigaban na su ya ginu ne akan ƙasusuwanmu da jininmu ne, don haka ɗan abinda ake gani suna da shi ba don mu ba to yanzu suna rayuwane cikin kwatami da caɓalɓali irin yadda suke kasance da suna rayuwa a baya, a saboda da haka cigabanmu yana ratayene

  • *Karatun Littafin* *نبي الرحمة سيرة ودروس وعبر* Drs na 58 *Mal. Abdurrahman Muhd Sani Umar* Daga Masallacin Markazul Imamul- Bukhari Rijiyar Zaki Kano. 04/08/2026 - 20/02/1448 - Daga cikin Darussan Hijira: Sunnar gwagwarmaya tsakanim gaskiya da karya. - babban ƙalubalen da ke gaban mai da'awa ko mai son kawo gyara Domin samun karatukan malam ku bibiyi waɗannan shafuka:* Whatsapp: (A) https://chat.whatsapp.com/EYip4EPotboLSTwqiPKkfv (B) https://chat.whatsapp.com/LvMW02BVKegCbubI7E3ZbS?mode=wwc Telegram: https://t.me/Abm_Sani Facebook: https://www.facebook.com/am.sani3?mibextid=ZbWKwL YouTube: https://youtube.com/@abdurrahmanmuhammadsani7823?si=SqgPVhLHWJTTBRIm

  • "A duniya, Allah yana ɗaukaka mai adalci, ko da kafiri ne. Kuma yana ƙasƙantar da azzalumi, ko da Musulmi ne. A Lahira kuma, Allah yana ɗaukaka mai tauhidi a kan kafiri. Domin haƙƙin Allah yana jinkirta sakamakonsa, amma haƙƙin mutum yana gaggauta sakamakonsa." Shekh Abdul'Aziz Attarify.

  • 2 August 2024: Zalincin shugabanni ba ya halatta zalincin talakawa, ko da kuwa shugabannin sune babban dalilin faruwar haka, shiyasa a lahira yadda Allah zai azabtar da manya masu faɗa a ji wataƙilama azabarsu ta zama ninki biyu haka zai azabtar da mabiya da masu rauni, saboda kowa aikinsa zai girba, sakamakon ɗayane saboda ma'aunin ɗaya ne. ⚖️🌍

  • Ana ba da labarin cewa Musaylimatul Kazzab, idan ya ratsa ta ƙasar da ke cike da korayen ciyayi, sai su bushe. Idan ya yi tofi a cikin rijiya, sai ta ƙafe. Idan kuma aka kawo masa wani mara lafiya ya yi masa addu'a ko ya yi masa tofi don neman waraka, sai ya mutu. Duk da irin waɗannan abubuwan amma mabiyansa suna ɗaukar hakan a matsayin nasarori !! Saboda haka, kada ka yi mamaki idan a yau ka ga wani shugaba yana jefa al'umma cikin wahala da masifu, yana tafka ɓarna, amma duk da haka a samu waɗanda za su riƙa kiran hakan da "achievements", suna yabonsa, har ma suna neman a ƙara ba shi dama ya ci gaba da irin wannan ɓarnar !!

  • Ga masu halatta cin mutuncin mutane da sunan haka siyasa take: Duk sanda aka shiga ba wa laifi kariya bisa hujjar cewa "haka ake yi" ko "haka aka saba", to babu ranar samun gyara kuma. Domin hakan tamkar an riga an shar'anta laifin ne, an kuma halatta shi. Shar'anta laifi da barna ya fi hatsari fiye da aikata laifin kansa. Don haka, fadin cewa "an saba da abu kaza" ko "haka dai yake" ba hujja ba ce a gaban Allah. Duk wanda yake ganin haka, ya shirya amsar da zai bayar a gaban Allah.

  • *Karatun Littafin* *الأربعون النووية* Drs na 60 *Mal. Abdurrahman Muhd Sani Umar* Daga Masallacin Imamu Musulim, Ɗanbare Unguwar katako, Kano 15/02/1448 30/07/2026 Hadisi na 19 * Darrussa dake cikin hadisin . *Domin samun karatukan malam ku bibiyi waɗannan shafuka:* Whatsapp: (A) https://chat.whatsapp.com/EYip4EPotboLSTwqiPKkfv?mode=wwt (B) https://chat.whatsapp.com/LvMW02BVKegCbubI7E3ZbS?mode=wwc Telegram: https://t.me/Abm_Sani Facebook: https://www.facebook.com/am.sani3?mibextid=ZbWKwL YouTube: https://youtube.com/@abdurrahmanmuhammadsani7823?si=SqgPVhLHWJTTBRIm

  • "Shaiɗan ya ci ƙarfinsu, sai ya mantar da su ambaton Allah." (Almujadila: 19) Abu na farko da Shaiɗan yake ɗaure mutum da shi shi ne hana shi ambaton Allah. Idan ya yi nasarar ɗaure harshensa daga zikiri, to sauran gabobinsa za su miƙa wuya gare shi. Shekh Abdul'Aziz Attarfy

  • *Karatun Littafin* *نبي الرحمة سيرة ودروس وعبر* Drs na 57 *Mal. Abdurrahman Muhd Sani Umar* Daga Masallacin Markazul Imamul- Bukhari Rijiyar Zaki Kano. 28/07/2026 - 13/02/1448 - Wasu al'amura da suka faru da Annabi (SAW) akan hanyarsa ta zuwa Madina. - Isowar Annabi (SAW) zuwa garin Madina da kuma yadda Al'ansar suka tarbe shi. Domin samun karatukan malam ku bibiyi waɗannan shafuka:* Whatsapp: (A) https://chat.whatsapp.com/EYip4EPotboLSTwqiPKkfv (B) https://chat.whatsapp.com/LvMW02BVKegCbubI7E3ZbS?mode=wwc Telegram: https://t.me/Abm_Sani Facebook: https://www.facebook.com/am.sani3?mibextid=ZbWKwL YouTube: https://youtube.com/@abdurrahmanmuhammadsani7823?si=SqgPVhLHWJTTBRIm

  • без подписи

  • *Karatun Littafin* *الأربعون النووية* Drs na 59 *Mal. Abdurrahman Muhd Sani Umar* Daga Masallacin Imamu Musulim, Ɗanbare Unguwar katako, Kano 08/02/1448 23/07/2026 Hadisi na 19 * Kasan Allah cikin yalawa zai san da kai lokacin tsanani * Nasara tana tare da haƙuri. * ƙunci da musiba suna tare da sauƙi da yaye musiba. *Domin samun karatukan malam ku bibiyi waɗannan shafuka:* Whatsapp: (A) https://chat.whatsapp.com/EYip4EPotboLSTwqiPKkfv?mode=wwt (B) https://chat.whatsapp.com/LvMW02BVKegCbubI7E3ZbS?mode=wwc Telegram: https://t.me/Abm_Sani Facebook: https://www.facebook.com/am.sani3?mibextid=ZbWKwL YouTube: https://youtube.com/@abdurrahmanmuhammadsani7823?si=SqgPVhLHWJTTBRIm

  • *Karatun Littafin* *نبي الرحمة سيرة ودروس وعبر* Drs na 56 *Mal. Abdurrahman Muhd Sani Umar* Daga Masallacin Markazul Imamul- Bukhari Rijiyar Zaki Kano. 21/07/2026 - 06/02/1448 * Fitowar Annabi (SAW) da nufarsa garin Madina. - Haɗuwar Suraqah bin Malik da Annabi (SAW) da abinda ya gudana tsakaninsu. Domin samun karatukan malam ku bibiyi waɗannan shafuka:* Whatsapp: (A) https://chat.whatsapp.com/EYip4EPotboLSTwqiPKkfv (B) https://chat.whatsapp.com/LvMW02BVKegCbubI7E3ZbS?mode=wwc Telegram: https://t.me/Abm_Sani Facebook: https://www.facebook.com/am.sani3?mibextid=ZbWKwL YouTube: https://youtube.com/@abdurrahmanmuhammadsani7823?si=SqgPVhLHWJTTBRIm