tgindex
FISABILILLAH 🌿

FISABILILLAH 🌿

Статистика

"Duk Wanda ya yi nuni akan aikin alkhairi, to, yana da lada kwatankwacin Wanda ya yi aikin" https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/ https://t.me/Fisabilillaaah

Последний пост
14 авг.
Последнее чтение
15 авг.
Постов за неделю
2
Всего постов
23
Тип
открытый
Язык
ha
Категория
Видео (по похожим)
В каталоге с
13 авг.
Подписчики
9 333
−14 за 4 дн.
Сутки
−5
−0,05%
Неделя
 
Месяц
 
Просмотров на пост
740
23 постов
Вовлечённость
7,9%
к подписчикам
Постов в день
0,3
всего 23
Упоминаний
0
каналов
Охват размещения
оценка
1/24сутки в ленте
136
1/48двое суток
155
1/72трое суток
168

Оценка по просмотрам недавних постов: пост набирает почти всё за первые сутки.

Посты

  • KYAUTATA NIYYA SHINE HANYAR TSIRA Shaykh Abdurrahman As-Si'idi Allah ya masa rahama yana cewa; "Babu wata hanyar rabauta face tsarkake niyya acikin bautar mahalicci, da kuma kokari wurin amfanar da bayinsa, duk wanda yayi dace da wannan hakika ya samu babban kaso na jindadi da tsira da rabauta". تيسير الكريم الرحمان ٥٧٥ #Zaurenfisabilillah Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

  • KADA KA BARI SHAIƊAN YA MAKA BUƘULU Shaikh Saleeh Fauzan Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana yake cewa: "Da yawa acikin mutane akwai waɗanda shaiɗan yake shagaltar dasu daga faɗin *{LA ILAHA ILLALLAH}* basa faɗanta sai jifa-jifa, basa ambaton Allah da ita sai ɗan kaɗan duk da gashi cewa tana da nauyi a mizani, kalmace mai girma, amma kadanne waɗanda su ke faɗakuwa gare ta kuma su ke faɗinta su ke sabarwa harsunan su furtata da maimaita ta, sai dai yan kaɗan daga cikin mutane keyin hakan". شرح رسائل اﻹمام المجدد | تفسير كلمة التوحيد ٧٧ #Zaurenfisabilillah TELEGRAM, https://t.me/Fisabilillaaah

  • *GIYACE TA SHAIDAN* Yahaya bn Mu'az (R) yace; "Duniya giyace ta shaidan, duk wanda ya bugu da ita zai wayi gari acikin sansanin matattu yana mai nadama atsakanin masu hasara." صفة الصفوة(٢٩٧/٢) #Zaurenfisabilillah Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah Instagram: https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/

  • MAFI GIRMAN ALAMUN NAGARTAR MACE SHINE KAMEWAR TA, SHI YA SA DUK DA YAWAN IBADAR MARYAMU YAR IMRANA ALLAH BA SHI YA FARA YABONTA DA SHI BA , DA KAMEWAR TA YA FARA. ومريم ابنة عمرن التي أحصنت فرجها MA'ANA MARYAMU YAR IMRANA WADDA TA KIYAYE AL'AURAR TA. FARKON ALAMUN NAGARTAR MACE: KAMEWAR TA. IYAYE A KULA MASU AURE A KULA. Dr. Usman Giade #Zaurenfisabilillah Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah Facebook: https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/

  • *KADA SHAIDAN YA RUDE KU!* Ibnul Jawzi, Allah ya yi masa rahama yana cewa: “Kuma daga cikin ruɗin shaidan akan gama garin mutane idan sun yi zunubi, sai aka gaya musu (kuskuren su) sai kaji suna cewa: "Ubangijinmu Mai karamci ne, kuma gafararSa mai yalwa ce." [Tablis Iblis] #basa tunawa da girman uqubarSa sai su fake da yalwar rahamarSa suyi ta sa6a maSa suna ketare iyakokinSa. #Zaurenfisabilillah Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah Instagram: https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/

  • 3 авг.4731из Fisabilillaaah

    *KA FADI GASKIA* Ibn Kathir (Rahimahullah) yana cewa: “Idan aka tambayeka game da wani al’amari, toh ka fadi gaskiya akansa, koh da kuwa zaka cutu. Domin Allah zai sanya mafita ga waɗanda suka yi maSa ɗa'a." [Tafsir Ibn Kathir, ayata 2 shafi na 434] #Zaurenfisabilillah Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah Instagram: https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/

  • TALALA CE Idan Allah Yayi fushi da bawa, Ya kuma yanke alaqa dashi kuma ta6ewa ta tabbata akan shi, sai Allah Yayi ta 6uda masa acikin harkokin sa. Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Idan kaga Allah (SWT) Yana bawa mutum walwala da wadata a rayuwar duniya alhali shi mai sa6a masa ne, toh talala Allah yayi mishi." [Al musnad Imam Ahmad : 16673] Allah Madaukaki Ya fadi acikin suratul An'am cewa: *"Sa´an nan kuma a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka bũɗe, a kansu, ƙõfõfin dukkan kõme, har a lõkacin da suka yi farin ciki da abin da aka ba su, Muka kãmã su, kwatsam, sai gã su sun yi tsuru tsuru."* [An'am : 44] Wani daga cikin magabata yana cewa: Sau da yawa akwai wadanda aka yi musu talala da ni'imomin da Allah ya musu amma basu sani ba. #Zaurenfisabilillah Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah Instagram: https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/

  • 27 июл.61320из daruAhlulquran

    " Godiya ta tabbata ga Allah swt ɗin da ya yaye mana baƙinciki. Dama dai ubangijin nan namu, ai mai yawan gafara ne da kuma tausayi. Haka ƴan Al-janna za su faɗa, bayan sun shiga Al-janna ɗin. ------------------------------------ Allah ka sanya mu cikin Aljannah, da iyayenmu da zuriyarmu duka.

  • *KADA KAYI WA MATARKA BARAZANA DA SAKI* Shaikh Ibnu Uthaimeen Allah ya masa rahama yake cewa "Kada ka yarda ka ambata wa matarka kalmar saki, domin alokacin da mutum ya ambata wa matarsa saki (da sunan barazana) to kalmar zatayi tayi mata yawo acikin zuciyarta, zatayi ta tunanin kalmar a bacci ko farke, wanda wannan babban kuskure ne, shiyasa yana daga cikin wauta mutum ya ambata wa matarsa saki koda kuwa dan tsoratarwa ne, ya kai ɗan uwa kamata barazana da wani abu amma banda saki. Idan ka mata barazana da saki shikuma shaiɗan zaita kaikoma acikin zuciyarta yana aiki akan wannan kalmar wadda aƙarshe sai ya zartar da wannan rabuwan a tsakanin ku, Allah ya tsare". اللقاء الشهري ٣١ #Zaurenfisabilillah https://t.me/Fisabilillaaah

  • 🍃🌸 *FALALAN ZUWA SALLAN JUMA'A DA WURI* Daga Sahabi Abi Huraira R.A Manzon Allah (SAW) ya ce;  "Idan ranar juma'a ta zo, Mala'aiku suna tsayawa akan kofar masallaci suna rubuta na farkon zuwa da mai bin shi, kwatankwacin Wanda ya yi sammako, kamar kwatankwacin Wanda ya bada sadakan Rakumi, Sannan kamar Wanda ya bada Saniya, sannan Wanda ya bada Rago, sannan (kwatankwacin Wanda) ya bada Kaza, se Wanda kamar sun bada sadakan Kwai, Idan Liman yazo se su nad'e takardunsu, se suje su saurari Khuduba. -Bukhari da Muslim suka ruwaito, (Dariqus-salihin 77pg) Note: ●Dukkanin wannan falalan (kwatankwacin ladan) za'a bada ne ga Wanda yaje kafin Liman yaje ne. Iya sammakan ka iya shagalinka. ●Idan Liman ya fara Khuduba, ba'a magana, ba'a cewa wani ya yi shiru idan yana yi. Ba'a wasanni (latsa) waya Ds.. Wanda ya aikata hakan ba shi da juma'a (falalan da ake samu na sallan juma'a). Kadai ana yin shiru a dakatar da komai a saurari Hud'uba Allah Ta'ala ya temake mu. #Zaurenfisabilillah https://t.me/Fisabilillaaah

  • без подписи

  • 🍃🤍🍃 *JUMU'A* Mu yawaita salati gare shi Sallallahu alaihi wa sallama. Manzon Allah (SAW) ya ce a yawaita salati gareshi daren Jumu'a da ranan Jumu'a. Ibnul Jauzi Allah ya masa rahama yake cewa: "Idan Allah yana son bawa da Alkhairi sai ya yassarewa Harshensa yawaita salatin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama". بستان الواعظين ١/٣٠٠ اللهم صل على محمد وعلى آل محمد كما صليت على إبرهيم وعلى آل إبرهيم إنك حميد مجيد، وبارك على محمد وعلى آل محمد كما باركت على إبرهيم في العالمين إنك حميد مجيد. #Zaurenfisabilillah https://t.me/Fisabilillaaah

  • WASIYYAR SAHABBAI GA JUNANSU Abu Madinat Ad-Darimi Allah ya masa rahama yana cewa: "Mutane biyu daga cikin sahabbai idan suka hadu ba zasu rabu ba face daya daga cikinsu ya karantama ɗan uwansa *SURAH AL-ASR* Sannan ma su yiwa junansu sallama". المعجم الأوسط ٥/٢١٥ *سورة العصر* والعصر* إن الإنسان لفي خسر* إلا الذين آمنوا وعملوا الصالحات وتواصو بالحق وتواصو بالصبر. SURAH AL-ASR: 1. Allah yana rantsuwa da lokaci/zamani. 2. Lalle mutum yana cikin hasara. 3. Sai dai kadai wadanda suka yi imani kuma suka yi aiki na kwarai, Sannan suka yi wasiya da gaskiya kuma suka yi wasiya da hakuri. #Zaurenfisabilillah TELEGRAM: https://t.me/Fisabilillaaah FACEBOOK: https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/

  • *A QONASHI* Sheikh Uthaymeen (R) yana cewa: “Ina nasiha ga ‘yan uwana masu jefar da takarda, da su dinga dubawa kafin su jefar. Idan suka ga aya ko hadisi daga Manzon Allah (ﷺ) ajiki toh su qona kada su jefar. Kuma su dinga kulawa sosai kada suyi sakaci da hakan." فتاوى نور على الدرب (٢/٥) #Zaurenfisabilillah Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah Instagram: https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/

  • 🥀🥀___ Ibnul-Qayyim (R) ya ruwaito daga Jariri cewa: “An bani labarin wani mutum daga Banu Isra’ila wanda yake da wata bukata da yake so Allah ya biya masa.  Don haka, sai ya shagaltu acikin yin ibada sannan kuma yana mai rokon Allah Ya biya masa bukatarsa.  Lokacin da bai ga cewa bukatarsa ta biya ba, sai ya kwana yana zargin kansa, yana cewa: “Ya kai!  Me ke damunka wanda yake hana a biya maka bukatunka? ” (wato yana tambayar kansa kenan) Sai ya kwana acikin bakin ciki yana mai tuhumar kansa, yana cewa: "Tallahi, matsalar ba ta kasance daga Ubangijina ba. Hakika dalilin rashin samun biyan wannan bukatar tawa tana tattare dani.," kuma ya kasance cikin irin wannan halin na ɗora wa kansa alhakin (rashin samun biyar bukatar) har sai da a  ƙarshe ya samu biyan buƙatarsa." 📖Ighasatul-Lahfan' (1/77) 'Yan uwa mu dage da yawan tuba da komawa ga Allah. Sau da dama silar rashin samun biyan bukatun mu suna tattare damu. #Zaurenfisabilillah Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

  • 6 июл.1 0239

    KADA KA YANKE ƘAUNA DAGA RAHAMAR ALLAH 💧Ibnul Jauzi Allah ya masa rahama yana cewa; "Kada ka yarda kana ganin tsayin lokacin bala'i har takai ka gajiya da yawan addu'a, domin kai an jarrabeka da wannan bala'inne, sai kuma aka bautar dakai da hakuri, dan haka kada ka yanke kauna daga rahamar Allah koda kuwa bala'in ya jima" ...صيد الخاطر ص439 #Zaurenfisabilillah TELEGRAM: https://t.me/Fisabilillaaah

  • 23 июн.1 23882из Fisabilillaaah

    KA GAMSU DA RABON DA ALLAH YA BAKA Hasanul-Baṣri (Allah ya yi masa rahama) yana cewa: "Duk wanda ya gamsu da rabon da Allah Ya raba Ya bashi, toh Allah zai wadatar masa kuma zai albarkace shi (acikinsa), amma wanda bai gamsu (da abunda Allah Ya raba Ya bashi ba), to Allah ba zai wadatar da shi acikin sa ba kuma ba zai sami albarkarsa ba." [Kitabul-Riḍā ʿan Allāh bi Qaḍāʾihi 95] #Zaurenfisabilillah Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah Instagram: https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/

  • 20 июн.1 2212из Fisabilillaaah

    AZUMIN TASU'A DA ASHURA TASU'A: Shi ne Azumin ranar Tara ga watan Muharram, an shar'anta shi ne dan saɓawa Yahudawa, Manzon Allãh (SAW) yana cewa, Idan Allah ya rayani zuwa shekara mai zuwa zan azumci ranan tara ga wata. - Muslim (1134) ASHURA: Manzon Allah (SAW) Ya ce game da Azumin ranan goma ga watan Muharram (Ashura) ina kyautata tsammanin a wurin Allah da ya kankare zunuban shekarar da ta gabace shi. - Muslim (1162). Allah Ta'ala ya bamu ikon Azumta #Zaurenfisabilillah Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

  • 16 июн.1 28513

    WATAN ALLAH MUHARRAM Ibnu Rajab Allah ya masa rahama yana cewa; "Haƙiƙa Annabi Muhammad (SAW) ya ambaci watan Al-Muharram da watar Allah, saboda girmanta da falalarta, domin Allah baya jingina wani abu gareshi sai abunda yake da daraja acikin halittunsa, kamar yadda ya jingina Annabi Muhammad da Annabi Ibrahim da Annabi Ishaq da Annabi Yaqub da sauran Annabawa zuwa ga bautarsa". لطائف المعارف 💧MUHARRAM yana cikin watanni hudu masu alfarma, Imamul Qurdibi R. Yace: "Allah ya keɓance watanni huɗu masu alfarma ne da ambato da kuma Hani da yin zalunci a cikin su, saboda girman sha'anin su duk da cewa zalunci haramunne a kowane lokaci. 💧Jamhur din malamai da imamai guda uku Abu Hanifa, Malik da Shafi'i duk sun tafi akan mustahabbine (anso) mutum ya yawaita azumi acikin su waɗannan watanni guda hudu, ya kuma ƙara kaimi a cikin musamman MUHARRAM da Rajab. #Zaurenfisabilillah 28/12/1441 18/8/2020 Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

  • 14 июн.1 0343из Fisabilillaaah

    WANE TANADI KA YI MA KANKA GAME DA SADAKA MAI GUDANA?? 💧Sahabi Abi Huraira ya ruwaito hadisi daga Manzon (SAW) yana cewa: "Lallai yana daga cikin abinda yake riskar mumini na aikin sa da ladarshi bayan mutuwar shi; ● Wani ilmi da ya koyar da shi, kuma ya yaɗa shi. ● Da Ɗa nagari da ya bari. ● Da kuma wani Alqur'ani da ya gadar da shi. ● Ko kuma wani masallaci daya gina. ● Ko wani gida ga matafiya da ya gina shi. ● Ko wata ƙorama da janyo. ● Ko wata Sadaqa da ya fitar da ita daga cikin dukiyarsa, a lokacin lafiyar shi, a halin rayuwar shi. To, wannan duka zasu riske shi a bayan rayuwar shi. Ibn Majah, kuma Al-baniy ya ingantashi. Duba (Dariqus salihin) Note: • Sadaqa mai gudana (Sadaqatu Jariya) shine duk wani aiki da ladan sa bazai yanke maka ba har bayan ka mutu. • Malamai suka ce fadin Manzon Allah (SAW) "ko wani ɗa na gari" . Ai idan ka dace da ɗa nagari da yake aikata alkhairi zaka rika samun lada. • "Ko wani Alƙur'ani da ya gadar" ma'ana, ya rubuta wani mus'hafi na Alqur'ani ya barshi ake karantawa, ko ya saya ya bayar, ko mutum ya bar nashi aka dauka ake karantawa. Zai rika samun lada. Allah Ta'ala  ka azurtamu da ayyukan alkhairi da zamu riƙa samun ladan su bayan rayuwar mu. #Zaurenfisabilillah https://whatsapp.com/channel/0029Va54zoM2f3EGKKcyG33Z