tgindex
BINTUS-SUNNAH

Domin Faɗakarwa da Tunatarwa Zuwa Ga Al'ummah Ta Fannoni Daban-Daban. TELEGRAM: https://t.me/BINTUSSUNNAH FACEBOOK: http://www.Facebook.com//Bintusunnah/ YouTube: https://youtube.com/channe WHATSAPP: http://api.whatsapp.com/send?phone=+2349030947171

Последний пост
15 авг.
Последнее чтение
15 авг.
Постов за неделю
39
Всего постов
39
Тип
открытый
Язык
ha
Категория
Видео
В каталоге с
13 авг.
Подписчики
3 759
−12 за 3 дн.
Сутки
−2
−0,05%
Неделя
 
Месяц
 
Просмотров на пост
54
39 постов
Вовлечённость
1,4%
к подписчикам
Постов в день
5,6
всего 39
Упоминаний
0
каналов
Охват размещения
оценка
1/24сутки в ленте
72
1/48двое суток
82
1/72трое суток
88

Оценка по просмотрам недавних постов: пост набирает почти всё за первые сутки.

Посты

  • MACE TA GARI ITA CE NUTSUWAR MIJINTA 🤍 Mace ta gari ba kawai wadda take son mijinta a lokacin farin ciki ba ce. Ita ce wadda idan mijinta ya yi nisa, zuciyarta ta damu da shi; idan wani abu ya same shi, ta ji kamar nata ne; idan ya gaji, ta nemi hanyar da za ta sauƙaƙa masa; idan ya kwanta, ta so ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Tana yawaita masa addu’a, tana kula da jin daɗinsa, tana girmama shi, kuma tana ƙoƙarin mayar da gidansu wuri na “soyayya, rahama da natsuwa tare da fahimtar juna” ❤️ Domin kyakkyawar mace ba wai wadda ake gani da ado kawai ba ce; “kyawun mace na gaske yana bayyana ne a yadda take kula da zuciyar mijinta.” 🌹 🤍 Rᵉᵉᵈᵉʳᵗ

  • ALHAMDULILLAH Ƴan'uwa barkanku da dare mun gode da ƙoƙarinku da kulawarku, an samu wasu daga cikinmu sun amsa TAMBAYARMU kuma duk sun bada amsa daidai, ALLAH Ya saka muku da alkhairi 🤲🏼 ✅ Amsar Tambayarmu shine: (B) Ya zauna da ita cikin kyakkyawar mu’amala. ƘARIN BAYANI: Mun samu amsarmu daga cikin Alƙur'ani Maigirma, ALLAH (ﷻ) Ya ce: «وَعَاشِرُوهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۚ فَإِن كَرِهْتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَيَجْعَلَ اللَّهُ فِيهِ خَيْرًا كَثِيرًا» Ma'ana: “Kuma ku yi musu kyakkyawar mu’amala. Amma idan har kun ƙi su, to mai yiwuwa ne ku ƙi wani abu, ALLAH kuma Ya sanya alheri mai yawa a cikinsa.” [Nisa'i: 19] Wannan aya tana koyar da maza wani babban darasi game da zamantakewar aure. Aure ba yana nufin mutum zai samu abokin zama wanda zai dace da dukkan abubuwan da yake so ba. Kowane mutum yana da halaye, rauni da ƙarfi. Saboda haka, idan miji ya ga wani hali a tare da matarsa halin da bai so, bai kamata ya gaggauta kallonta da ƙyama ko ya manta da dukkan kyawawan halayenta ba. ALLAH Ya tunatar da shi cewa wataƙila abin da yake ƙi yana ɗauke da wani alheri mai yawa da bai sani ba. Haka kuma wannan ba yana nufin mace ta ci gaba da aikata abin da yake cutarwa ko zalunci gare shi ba. A'a. Idan akwai matsala, ana neman gyara ta hanyar hikima, nasiha, haƙuri da kyakkyawar mu'amala. Abin lura shi ne, aure ba ya ginuwa kawai a kan soyayya da jin daɗi; yana buƙatar haƙuri, yafiya, mutunta juna da fahimtar juna. Wani lokaci mutum zai ga wani abu da bai so, amma daga baya sai ya gane cewa ALLAH Ya sanya alheri mai yawa a cikin wannan mutumin ko a cikin wannan yanayin. 💡 Darasin da za mu koya: Kada mu mayar da wani kuskure ko hali guda ɗaya ya sa mu manta da dukkan kyawawan halayen abokin zamanmu. Mu koyi ganin alheri, mu yi haƙuri, mu gyara abin da ya kamata a gyara, kuma mu barwa ALLAH abinda ba za mu iya canjawa ba. ALLAH Ya sanya gidajen Musulmai su kasance gidajen soyayya, rahama, haƙuri da zaman lafiya. Aameen. 🤲 ALLAH Shi ne mafi sani.

  • без подписи

  • без подписи

  • без подписи

  • UPDATE THIS WEEK !!!

  • без подписи

  • Soyayya ta gaskiya tana farawa ne da Tsoron ALLAH, Idan kaso mutum saboda ALLAH Toh ko Wane kalma ko Wane Aiki ko Wane lokaci Zasu Kasance masu tsarki, ka tuna Haƙuri da fahimta sune ginshiƙin soyayya Mai ɗorewa. kuma ko wacce kalma Mai kyau tana da lada a wajen ALLAH. Ku yi soyayya domin ALLAH, kuma kada ku manta da ALLAH a Kowane lokaci. Soyayyar da ALLAH Ya Aminta da ita, tana tsarkake zuciya, tana gyara Halaye, Kuma tana kawo farin ciki na gaskiya wadda ba ya gushewa. 🤍 Rᵉᵉᵈᵉʳᵗ

  • SURATUL KAHF !!! Akwai alƙawura guda biyu na musamman da aka haɗa da Suratul Kahf: Duk wanda ya karanta Suratul Kahf a ranar Juma’a, Allah zai sanya masa wani haske tsakanin Juma’a biyu. Kuma duk wanda ya haddace ayoyi goma na farkonta, za a kare shi daga fitinar Dajjal. (Muslim/Hakim) Suratul Kahf ta yi magana ne kan manyan fitinu guda huɗu da za su iya fuskantar mutane a ƙarshen zamani: fitinar addini, fitinar dukiya, fitinar ilimi, da fitinar iko. Kuma kariya daga kowace ɗaya daga cikin waɗannan fitinu tana cikin surar kanta. Allah Ya sanya karanta Suratul Kahf ya zama al’ada ta yau da kullum a gare mu. Amin. ✍️ SAFAR📚🖊️

  • 💚Jumu'at Checklist ✨

  • 01/RABI'UL AWWAL/1448 14/AUGUST/2026 ADDU’AR YAU JUMA'A: Ya ALLAH ka ɗaukaka musulunci da musulmai kuma ka sauƙaƙa mana hanyar fahimtar addinin musulunci kuma ka bamu ikon aiki da shi da kuma yaɗa shi. HADISIN YAU JUMA'A: An Karɓo daga Abu-hurayrah (RA) Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Lallai ne wannan addinin me sauƙi ne, kuma babu wanda zai tsananta cikinsa face addinin ya yi galaba kansa, saboda haka ku dai-dai tu, ku kusanci juna, kuyi bushara da aljanna, ku nemi taimakon ALLAH ta hanyar sammako da yammaci, da wani yanki na dare.” [Bukhari ya ruwaito shi] Telegram https://t.me/BINTUSSUNNAH Facebook http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

  • без подписи

  • без подписи

  • Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarkatuhu TODAY IS FRIDAY 1 RABI'UL AWWAL 1448H, 14 AUGUST 2026 May ALLAH accept our righteous deeds during Ramadan and beyond. May ALLAH enable us to fulfill our daily Ibadats, accept them, and reward us with Jannatul Firdaws.

  • без подписи

  • без подписи

  • без подписи

  • Yawancin mutanen da suke samun wahalar karatun Alƙur’ani suna jin kunyar yadda suke karantawa. Amma wannan Hadisin yana gyara wannan tunanin. Annabi (ﷺ) Ya ce: “Wanda yake karanta Alƙur’ani cikin ƙwarewa, zai kasance tare da mala’iku maɗaukaka masu biyayya. Amma wanda yake karanta Alƙur’ani yana fama da wahala, yana tuntuɓe-tuntuɓe wajen karatunsa, yana da lada sau biyu.” [Bukhari da Muslim] Ba rabin lada ba ne saboda wahalar karatun. Lada biyu ne: ● Lada ɗaya saboda karatun Alƙur’ani. ● Lada ɗaya saboda ƙoƙarin da yake yi da wahalar da yake jurewa. Don haka, ka isar da wannan saƙon ga duk wanda yake jin kunyar yadda yake karanta Alƙur’ani. Kada ya ji kunya. Ya ci gaba da karatu. Wahalar da kake sha a kan karanta Alƙur’ani ba asara ba ce; lada ce. ✍️ SAFAR📚🖊️

  • без подписи

  • 29/SAFAR/1448 13/AUGUST/2026 ADDU’AR YAU ALHAMIS: Ya ALLAH tsaremu da yin rantsuwa a kan ƙarya, kuma ka raba mu da yin zalunci a rayuwarmu. HADISIN YAU ALHAMIS: Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: "Wani mutum ba zai yanke (wato ya karɓi) haƙƙin mutum musulmi da rantsuwar ƙarya ba, face sai ALLAH Ya wajabta wuta a kansa. Sai wani sahabi ya ce; ko da abin kaɗan ne? Sai Annabi (ﷺ) ya ce; ko da asuwakin itacen a'rik ne.” [Sahihu sunan ibn Majah: 1882, Ibn Majah: 2324] Telegram https://t.me/BINTUSSUNNAH Facebook http://www.Facebook.com//Bintusunnah/