TAMBAYA DA AMSA.
СтатистикаMun Buɗe wannan Channel ne domin Amsa Tambayoyin Al'ummar Musulmi baki ɗaya. Duk mai tambaya zaibi Admin ta private ya gabatar da Tambayarsa. فَسۡـََٔلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلذِّڪۡرِ إِن كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ "Ku Tambayi Ma'abota sani idan yazama baku sani ba"
- Последний пост
- 14 авг.
- Последнее чтение
- 13 авг.
- Постов за неделю
- 23
- Всего постов
- 28
- Тип
- открытый
- Язык
- ha
- В каталоге с
- 13 авг.
- 1/24сутки в ленте
- 31
- 1/48двое суток
- 35
- 1/72трое суток
- 38
Оценка по просмотрам недавних постов: пост набирает почти всё за первые сутки.
Посты
без подписи
без подписи
без подписи
без подписи
без подписи
без подписи
без подписи
без подписи
MATSAYIN MACEN DA TAKE YIN TIKTOK: : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Assalamualekum mallam ya matasayin mace take yin TIKTOK? : 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Wa alaikumus salam warahmatullahi wabarakatuh. Yin TikTok ba haramun bane kai tsaye, amma hukuncinsa yana dogara da abinda mace take yi da yadda take bayyana kanta. Idan tana yin abubuwa masu amfani, kamar koyarwa, nasiha ko yaɗa alkhairi kamar karatuttukan malamanmu na sunnah domin yan'uwa su karu, sannan ba tare da nuna tsiraicinta ba, ko yin ado domin jan hankalin maza, magana ko motsin da bai dace da Shari’a ba, ko yaɗa abubuwan haram ba, to asali ya halatta. Amma idan TikTok ɗin ya ƙunshi nuna tsiraici ko siffar jiki, rawa, kwaikwayo na batsa, jan hankalin maza da gangan, ko yaɗa abinda Shari’a ta haramta, to wannan baya halatta. Allah Maɗaukaki Yace: وَقُلْ لِّـلۡمُؤۡمِنٰتِ يَغۡضُضۡنَ مِنۡ اَبۡصَارِهِنَّ وَيَحۡفَظۡنَ فُرُوۡجَهُنَّ وَلَا يُبۡدِيۡنَ زِيۡنَتَهُنَّ اِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَا وَلۡيَـضۡرِبۡنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلٰى جُيُوۡبِهِنَّ وَلَا يُبۡدِيۡنَ زِيۡنَتَهُنَّ اِلَّا لِبُعُوۡلَتِهِنَّ اَوۡ اٰبَآٮِٕهِنَّ اَوۡ اٰبَآءِ بُعُوۡلَتِهِنَّ اَوۡ اَبۡنَآٮِٕهِنَّ اَوۡ اَبۡنَآءِ بُعُوۡلَتِهِنَّ اَوۡ اِخۡوَانِهِنَّ اَوۡ بَنِىۡۤ اِخۡوَانِهِنَّ اَوۡ بَنِىۡۤ اَخَوٰتِهِنَّ اَوۡ نِسَآٮِٕهِنَّ اَوۡ مَا مَلَـكَتۡ اَيۡمَانُهُنَّ اَوِ التّٰبِعِيۡنَ غَيۡرِ اُولِى الۡاِرۡبَةِ مِنَ الرِّجَالِ اَوِ الطِّفۡلِ الَّذِيۡنَ لَمۡ يَظۡهَرُوۡا عَلٰى عَوۡرٰتِ النِّسَآءِ وَلَا يَضۡرِبۡنَ بِاَرۡجُلِهِنَّ لِيُـعۡلَمَ مَا يُخۡفِيۡنَ مِنۡ زِيۡنَتِهِنَّ ؕ وَتُوۡبُوۡۤا اِلَى اللّٰهِ جَمِيۡعًا اَيُّهَ الۡمُؤۡمِنُوۡنَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُوۡنَ "Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyẽwa daga ƙawarsu. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo". (Surah: An-Noor, Ayat: 31). Saboda haka, ba TikTok ɗin kansa ne haram ba, sai dai abinda ake amfani dashi wajen yi ne yake sanya shi ya zama halal ko haram. Idan mace za tayi amfani da TikTok, ya kamata ta kiyaye sa hijabi, mutunci, magana mai kyau, da nisantar duk wani abu da zai jawo fitina ko lalata tarbiyya. Amma idan ta san cewa ba zata iya kiyaye waɗannan ƙa’idojin ba, ko kuma amfani da TikTok ɗin zai kai ta ga fallasa jikinta, yin abubuwan da basu dace da Musulunci ba, ko jawo mata fitina, to bai halatta tayi amfani dashi ta wannan hanyar ba. Musamman a wannan zamani da ake samun yawaitar lalacewar tarbiyya, ya kamata mace ta ƙara taka-tsantsan wajen abinda take kallo, abin da take wallafawa da kuma irin mutanen da take hulɗa dasu a kafafen sada zumunta (social media). WALLAHU TA'ALA A'ALAM Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. 𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G 𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇 Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇 https://t.me/TambayaDaAnsa ✍️𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏 𝐀𝐃𝐌𝐈𝐍 : 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟. +2348087788208 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
HUKUNCIN CIN NAMAN MAGE: : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Slm dan Allah malam mage ta halatta a addini aci ko bai halatta ba? : 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Wa’alaikumus salam. Cin naman mage baya halatta, a mafi yawan ra’ayin malamai dalili hakan itace hadisin Jabir رضي الله عنه cewa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya hana cin naman dabbobin farauta masu haƙora, kuma mage tana cikin dabbobin da suke da haƙoran farauta. Haka kuma, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana mage a matsayin dabbar da take yawan yawo a cikin gidaje, amma wannan ba yana nufin an halatta cin namanta ba. Malamai sun yi bayanin cewa mage tana cikin dabbobin da ba a yarda a ci namansu ba. Saboda haka, ba a halatta Musulmi ya ci naman mage ba, kuma ba a yanka ta domin neman nama. Amma idan an samu wani yanayi na larura ta gaske, hukuncin larura yana da nasa bayanin na musamman. WALLAHU TA'ALA A'ALAM ✍️MT ABDULLAHI Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. 𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G 𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇 Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇 https://t.me/TambayaDaAnsa ✍️𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏 𝐀𝐃𝐌𝐈𝐍 : 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟. +2348087788208 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
HUKUNCIN MAƊIGO: : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Assalamualaikum mlm fatan an wuni lfy mlm inada tambaya mlm akwai wata kawata da take cikin wani hali mlm tace Dan Allah menene makomarta ta aikata san zuciyarta ne taje wurin wata hajiya tayi amfani da ita mace da mace Wanda amma daga wannan Rana tayi nadama bakuma tasakeyi ba taji tsoron Allah yashigeta shine tace shin Allah zai karbi tuban ta ngd : 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh. A shari'ar Musulunci, madigo wanda ake kiran SIHAQ babban zunubi ne kuma laifi ne dake tattare da sauraran hukunce-hukunce na TA'AZEER (hukuncin da alkali ya yanke domin hana saɓo), domin babu takamaiman hukuncin Haddi da ya zo a Nassoshi kai tsaye kamar na zina. Saduwa tsakanin namiji da namiji (luwadi) ko saduwa tsakanin mace da mace (madigo) ko ta wani ɓangare saduwar ta kasance suka aikata ta gaba ne ko baya, shine mafi munin zunubi wanda saboda tsananin munanar sa har ALLAH ya hallaka al'umma akai, al'ummar Annabi luɗu (AS). Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace'; ALLAH ya la'anci duk wanda ya aikata aiki irin na mutanen Annabi luɗu (AS) Wato luwadi, har sau uku Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana maimaita wa. Ahmad ya ruwaito. Daga jabir Bin Abdillahi (RTA) Yace'; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: Lallai mafi tsoron abunda nake jiye wa al'umma ta tsoro, aiki irin na mutanen Annabi luɗu (AS) ! Wato luwadi. [Ibnu majah albani ya inganta]. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace'; Duk wanda kuka tarar yana aikata aiki irin na mutanen Annabi luɗu (AS), to ku kashe wanda ke aikatawan da wanda ake aikatawa da shi ɗin. Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) Yace "Idan Mace Tazo Ma Mace (Wato Sukayi Madigo) To Su Biyun Mazinata Ne". Madigo yana ɗaya daga cikin manyan laifukan da Ubangiji ya kyamata, sai dai shari’ah bata bada ainihin wani hukuncin da za’ayi wa masu madigo ba. Sai dai mafi yawan malamai suna ganin za’ayi masu hukunci dai-dai da na yan luwadi. wato kashe duk wanda ke aikatawan da wanda ake aikatawa da shi. Masana ilimin fiqihu sun tafi a kan cewa malami ko alkali yana da ikon yanke wa mai aikata madigo hukuncin bulala mai zafi, daurin kurkuku, ko kuma wulaƙantarwa domin ya azabtar da ita ta yadda za ta hana wani ko ita sake aikatawa. To ya zama wajibi gareta ta tuba kuma ta yawaita istigifari tare da nadama bisa abinda ta aikata, kuma ta nisanci duk wata kawarta ko wata hanyar da zata mayar da ita ga wannan dabi'a. Allah mai gafara ne mai jin qai. Yana karɓar tuban bayinsa aduk sanda suka tuba zuwa gareshi. Mutukar sunyi irin tuban da yake so. Ta yawaita ayyukan alkhairi tare da rokon gafarar Ubangiji mutukar tana raye aduniya. Domin bata da tabbacin shin Allah ya karɓi tubanta ne ko bai karɓa ba!!!. Don haka kada ta ɗauki abun kamar Qaramin abu. Anan nake jan hankalin 'yan uwa Mata cewa duk matar da tasan acikin Qawayenta akwai mazinata da 'yan madigo cewa ta nisancesu ta dena Qawance dasu. Domin Allah ya kawomu wani irin zamani wanda mutane basu ganin girman kowanne irin saɓon Allah mutukar zasu samu biyan bukata. Wajabi ne ga duk masu irin wannan dabi’ar ta madigo da suji tsoron Allah su nisantar da kan su ga barin yinsa. Su tuna ko wane lokaci za su iya riskar mahaliccin su bayan suna aika wannan mummunar aikin. Ya Allah muna tawassali da sunayen ka kyawawa da ka kiyaye mu da fadawa cikin wannan halin, ka shiryar da masu yi, ka gafarta mana ka kuma anshi tuban mu. Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum 🤲 WALLAHU A'ALAM Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. 𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G 𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇 Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇 https://t.me/TambayaDaAnsa ✍️𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏 𝐀𝐃𝐌𝐈𝐍 : 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟. +2348087788208 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
HUKUNCIN MALLAKAR ALƘUR’ANI GUDA BIYU DA AMFANI DA ƊAYA KAWAI: : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Assalamu alaikum barka da dare mallam Ina son sani in mutum nada Alkur'ani guda biyu yana karatun ɗaya ya ajeye ɗayan akwai laifi? : 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Wa’alaikumus salam warahmatullahi wabarakatuh. Babu laifi mutum ya mallaki Alƙur’ani guda biyu ko fiye da haka, ya kasance yana karatun ɗaya ya ajiye ɗayan. Alƙur’ani littafin Allah ne, kuma ba wajibi bane mutum ya riƙa karanta dukkan Alqur'anin ɗin da yake dashi. Abinda yafi muhimmanci shine ya girmama Alqur'anin, kada ya wulaƙanta su ko ya bar su a wurin da bai dace ba. Don haka mallakar Alƙur’ani biyu da amfani da ɗaya kawai ya halatta, babu zunubi sai dai ina mai baki shawara inda hali idan akwai wanda kikasan yana bukatan Al'qur'ani kuma bashi da halin mallakarsa ki bashi ɗayan fisabilillahi domin idan mutun ya karanta koda da harufa ɗaya ne kema kinada lada a wurin Allah WALLAHU TA'ALA A'ALAM ✍️MT ABDULLAHI Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. 𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G 𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇 Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇 https://t.me/TambayaDaAnsa ✍️𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏 𝐀𝐃𝐌𝐈𝐍 : 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟. +2348087788208 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
HUKUNCIN KUƊIN ZABIN DA YARINYA TA BARI BAYAN RASUWA: : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Assalamualaikum warahmatullah mlm brk da dare fatan ka wuni lpy Mlm tambaya ta shine yarinya ce ta mutu sai ta bar zabi guda hudu 4 sai akayi musu kudi dubu arba'in to mlm wa za'a bawa kudin tsakanin mahaifiyar ta da mahaifin ta? Ngd Allah ya sakawa mlm da alkairi : 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Idan yarinya ta rasu ta bar zabi huɗu da take kiwo, aka sayar dasu aka samu Naira dubu arba'in (₦40,000) to wannan kuɗin gadonta ne. Ba a ba mahaifi ko mahaifiya su kaɗai ba, sai dai a raba su tsakanin duk magadanta kamar yadda shari'ar Musulunci ta tanada bayan an biya duk wani bashi ko wasiyya data dace idan akwai. Idan magadanta su ne mahaifinta da mahaifiyarta kawai, kuma ba ta da miji, bata da ɗa, kuma babu wasu magada masu hana gado, to mahaifi zai karɓi kaso mafi yawa, mahaifiya kuma za ta karɓi rabonta na shari'a. Saboda haka, ba daidai bane a ba mahaifiya kaɗai ko mahaifi kaɗai kuɗin ba tare da an yi rabon gado bisa shari'a ba. Allah ya gafarta mata damu baki daya WALLAHU TA'ALA A'ALAM ✍️MT ABDULLAHI Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. 𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G 𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇 Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇 https://t.me/TambayaDaAnsa ✍️𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏 𝐀𝐃𝐌𝐈𝐍 : 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟. +2348087788208 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
HUKUNCIN WANDA YA SAKI MATARSA SAKI UKU, SAI YACE SAKI BIYU YAYI: : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Aslm allah ya karawa malan lfy da nisan kwana dan Allah malan ina tambaya menene hukuncin wanda yasaki matarsa saki 3 bayan kwana biyu sai yace saki biyu yai yana sane amman yace saki na 3 baya sane yayisa to malan ya lamarin auren yake ngd : 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Wa'alaikumun salamu warahamatullah, Idan mutum ya furta wa matarsa saki uku a lokaci guda ko a yanayi da yake tabbatar da cewa ya furta kalmomin sakin uku, sannan bayan kwana biyu yace Saki biyu yake sane dasu, amma na ukun ban sani ba cewa ya furta shi” to hukuncin yana buƙatar a duba ainihin kalmomin daya furta da kuma halin hankalinsa lokacin da yake furta sakin. Idan ya furta saki na uku ne cikin cikakken hankalinsa, yana sane da abinda yake faɗa, to rashin sanin cewa furta saki na uku zai iya jawo sakamakon saki uku ba yasa sakin ya zama biyu kawai. A irin wannan yanayin, idan an tabbatar da sakin uku, to aure ya ƙare da saki uku, kuma baya halatta ya sake aurenta sai tayi wani ingantaccen aure da wani namiji, sannan wannan auren ya ƙare bisa halal. Allah Maɗaukaki Yace: فَإِنْ طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُ مِنْ بَعْدُ حَتَّىٰ تَنْكِحَ زَوْجًا غَيْرَهُ Ma’ana: “Idan ya sake ta saki na uku, to ba ta halatta gare shi ba daga baya har sai ta auri wani miji.” — Suratul Baqarah ayata 230. Amma idan abin daya faru shine a lokacin furta saki na ukun bai san abinda yake faɗa ba saboda wani yanayi daya cire masa fahimta ko hankalinsa, to wannan yana da hukunci daban, kuma bai kamata a yanzun na yanke hukunci kai tsaye ba. Saboda haka, ya kamata mijin da matar da waliyyansu su kai wannan batu ga malamin daya ƙware a fikihu a inda suke ko kotun Shari'a, su bayyana masa kalmomin da aka furta daidai yadda aka faɗe su, sau nawa aka faɗe su, da kuma halin mutumin lokacin da yake faɗin su. Domin bambancin kalma ɗaya ko yanayin mutum na iya sauya hukuncin. WALLAHU TA'ALA A'ALAM ✍️MT ABDULLAHI Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. 𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G 𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇 Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇 https://t.me/TambayaDaAnsa ✍️𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏 𝐀𝐃𝐌𝐈𝐍 : 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟. +2348087788208 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
sukace bai halattaba, domin yazama kamar tayi auren Kisan-Wuta kenan, Sannan kuma gashi ta yaudari Mijin, ta cutar dashi, ta munana masa, dankawai yasaketa. Saidai Mafi yawa daga cikin Malamai sukace idan harMijinta nabiyun yasaketa to yahalatta takoma wajen Mijinta nafarko, sukace duk wanda igiyar aure ba ahannunsa takeba to niyyarsa ta rabuwa batada wani tasiri, domin bata da'ikon ta'iya sakin kanta dakanta dole sai ansaketa, Saidai abinda tayiwa Mijin na yaudara da munanawa sukace ananne takeda laifi, da kamata yayi ace tayi amfani da hanya maikyau wacce Mijin bazai cutu sosaiba, wato ta lallabashi har ya yarda suyi Khul'i ta mayar masa da Sadaƙinsa, hakan shiyafi dacewa. Don neman Ƙarin bayani sai aduba waɗannan Լitattafai kaMar Ӈaka:↓↓↓ " ﺷﺮﺡ ﻣﺴﻠﻢ " ( 3/10 ) " ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻱ ﺍﻟﻜﺒﺮﻱ " ( 6/298 ) " ﺍﻟﻤﻐﻨﻲ ﻹﺑﻦ ﻗﺪﺍﻣﺔ " ( 7/138 ) WALLAHU A'ALAM Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa... 𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G 𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇 Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇 https://t.me/TambayaDaAnsa ✍️𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏 𝐀𝐃𝐌𝐈𝐍 : 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟. +2348087788208 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
HUKUNCIN AUREN KISSAN-WUTA: : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Assalamualaikum warahamatullahi wabarkatuhu. yasayyadi. Barkada safiya. Hukunchin auren kisan wuta . Wanda akahada bakida . Amaryar da kuma mijinda sukarabu??? Masha Allah muna godiya sosai 🙏 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh. Ko-Shakka-Babu cewa auren Kisan-Wuta haramun ne, bai halatta ba, kamar yadda yazo acikin Hadisi Manzon Allah ( Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana cewa: " ﻟﻌﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻤﺤﻠﻞ ﻭﺍﻟﻤﺤﻠﻞ ﻟﻪ " ( ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ) "Abu dauda yaruwaito hadisi (2076) Annabi (Sallallahu Aaihi wasallam) ya tsinewa mai Auren Kisan-Wuta da wanda ya aura dan ta halatta gawanda yasaketa). Albani Ya Ingantashi Acikin sahihu Sunan Abu dauda. Allah maɗaukakin Sarki Yana cewa: فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُ مِن بَعْدُ حَتَّىٰ تَنكِحَ زَوْجًا غَيْرَهُ فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا أَن يَتَرَاجَعَا إِن ظَنَّا أَن يُقِيمَا حُدُودَ اللَّهِ وَتِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ يُبَيِّنُهَا لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ Sa'annan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'annan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cẽwa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani. (Suratul Baqara ayata 230). Danhaka kenan idan Mutum yasaki Matarsa har Saki(3) to bai Halatta yadawo da'itaba dole sai ta auri wani Mijin kuma ingantaccen aure, kuma bawai ya aureta bane da nufin nangaba yasaketa dan takoma wajen tsohon Mijintaba, Sannan kuma Sharaɗine yakasance Mijinda ta aura ɗin yataɓa Jima'i da'ita aƙalla koda sau ɗayane, to idan Mijin yarasu kokuma yasaketa dan raɗin kansa, to ya halatta takoma wajen tsohon Mijinta ya aureta, amma idan yazamana cewa Sabon Mijin da ta aura bai taɓa yin Jima'i da'itaba harsuka rabu dashi, to haryanzu batazama halal ga tsohon Mijintaba dole sai tasake wani auren kenan. Amma idan yakasance Mijin dayasaki Matar saki uku, dama sunhaɗa bakine dashi da wani abokinsa dakuma ita Matar akancewa shi abokinnasa ya Aureta inyaso daga baya sai yasaketa tadawo wajen tsohon Mijinta, to ko shakka babu cewa wannan haramunne kuma Kaba'irace daga manyan zunubai, Sannan kuma shi wanda ya aureta ɗin danufin haka aurensu da'itaɗin Ɓataccene a Shari'a, idanma yasadu da'ita to Zina kawai sukayi, hakanan kuma koda ya saketa to bai halattaba takoma wajen Mijinta nafarkonba, idankuma hartakoma yasake aurenta to su tabbata cewa zaman Daduro (zina) sukeyi. Amma idan shi wanda ya aureta ɗin babu wani haɗin baki dasukayi da tsohon Mijin nata wataƙilama shi tsohon Mijin nata baisanma cewa wannan ɗin zai auretaba, amma shikuma wanda zai aureta ɗin dama azuciyarsa yanaso kawai ya aureta dan yasaketa taƙara komawa wajen tsohon Mijinta, to shima aurensa da Matar Ɓataccen aurene sakamakon mummunar niyyarsa kuma shima in yasadu da'ita to zina kawai sukayi, danhaka shima koda yasaketa to bai halatta takoma wajen Mijinta nafarkoba. Amma Idan yakasance ita Matar dama azuciyarta tanasone ta auri wani danufin cewa idan suntare daga baya zatanemi yasaketa kokuma tayi ta munana masa haryagaji yasaketa, to anan sai Malamai sukayi Saɓani, Mazhabin HANABILA dakuma wasu daga cikin Malamai kamar irin su: Hasanul-Basriy, Ibrahimun-Nakh'iy, Shaikhul-Islam Ibn-Taimiyya, Sukace shima wannan nau'ine na auren Kisan-Wuta, danhaka shima bai halattaba sakamakon mummunar niyyarta, Sannan sukace idan ɗaya daga cikin su ukun (wato mijin ko matar kokuma shi wanda zai aura) yayi nufin ayi auren kuma daga baya asaketa takoma wajen nafarko, sukace duk hukuncinsu ɗayane auren baiyiba. Saidai Mazhabin MALIKIYYA dakuma wani sashe na HANABILA sukace idan har yasaketa to ya halatta takoma wajen tsohon Mijinta sukace niyyarta na auren Kisan-Wuta batada wani tasirin da zata ɓata aurensu, Saidai wasu daga cikin Ma'abota Ilimi sukace Maganar farko tafi ƙarfi, tunda asali bai halatta takomaba harsai tayi ingantaccen aure, amma yanzu taje tayine da nufin nangaba takashe auren awani lokaci sananne
Abu zarrin RA ya ruwaito, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: Idan kuka sadu (jima'i) da iyalanku za a baku lada, sai sahabbai suka ce, yaya ɗayanmu zai biya sha'awar sa kuma a bashi lada? Sai yace ku bani labari, idan yayi zina ba za a rubuta masa alhakki ba? Sai suka kwarai, sai yace to haka za a bashi lada idan ya kwanta da iyalansa. Muslim 1006. Abu Dauda 1286. Abdullahi ɗan Masud yana cewa Da zai zama saura kwana ɗaya duniya ta tashi, zan so ace nayi aure a wannan lokacin (Musannnaf Ibn abi Shaibah 3/454 ). Ibn Abbas R.A, sahabin Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Yace "Ku yi aure, domin kwana guda da aure shi ne mafi alheri daga ibadar shekara dubu". Waɗannan hadisan akwai su cikin Buguyatul Muslimina. Fa’idodin da suke cikin aure ba za su Kididdigu ba amma ga wasu kaɗan daga ciki za mu lissafo kamar haka; 1. Yin aure biyayya ne ga Umurnin Allah da Manzon Allah (Sallallahu Alaihin Wasallam). 2. Yin aure yana sanya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) farin ciki a ranar lahira. Yace “Ku yi aure ku hayayyafa domin ni zan yi ma sauran al’ummomi alfahari da ku a ranar Alkiyamah”. 3. Ta dalilin aure za ka samu wanda zai fito ta jikin ka, har ya girma yana kalmar Shahada!! 4. Ta dalilin aure ne za ka samu zuriyar da za su yi maka addu’a bayan rasuwar ka wannan yana daga cikin ayyukan da ladan su ba zai yanke ba har abada. 5. Yin aure ya kan zama dalilin runtsewar idanun mutum daga kalle kallen haramun, sannan ya kare masa al’aurar sa daga Zina. 6. Ta dalilin aure ne za ka samu damar taimaka ma ƴar uwar ka Musulma, ka aure ta, ka kiyaye ta kenan daga Zina. 7. Ta dalilin aure ne za ka samu cikar Addinin ka, da ninkawar ladan ka fiye da wanda ba su da aure. 8. Ta dalilin aure ne za ka samu ladan ciyar da Matar ka, da daukar nauyin ta, da ladan samar mãta da Mazaunin da za ta rayu. 9. Ta dalilin aure ne za ka samu damar Qara yawan Musulman duniya ta hanyar haihuwar da za ka samu. 10. Ta dalilin aure ne za ka samu damar karkatar da himmar ka daga kan nemen biyan bukatar ka ta hanyar haram izuwa ga hanyar halal. Da kuma samun ladan saduwa da iyalan ka. 11. Za ka samu lada mai girma sosai idan har Allah Ya azurta ka da ƴa’ya mãta guda biyu, kuma kayi hakuri da su ka kyautata musu, ka kyautata tarbiyyar su, su za su zama garkuwar ka daga shiga wuta. 12. Idan har ƴa’yan ka guda biyu suka rasu, kuma kayi hakuri, toh Allah zai shigar da kai Aljannah saboda wannan. 13. Ta dalilin aure za ka samu Qaruwar mutuncin ka da darajar ka a cikin al’ummah, ka shiga sahun mutanen da za su iya jagorantar lamuran rayuwar al’ummah. 14. Ta dalilin aure ne zaka samu taimakon Allah cikin lamarin ka. Kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Yake cewa: mutum uku, hakki ne akan Allah ya taimake su. ① wanda zai yi aure don nufin kame mutuncin sa. ② bawa wanda yake neman ‘yancin sa saboda ya samu daidaituwa (a cikin addini). ③ mujahidi (mai yakin daukaka addinin Allah). Muna tunatar da matasa da ƴan mata da suke da ikon yin aure, lallai a je ayi aure, a rage burin duniya. Kullum rayuwa tafiya take yi mutuwa zuwa yake yi babu notice, ku dubi duk waɗannan garaɓasar amma ban da Tuzurai da Gwagware Mãta da Mazã, su ba za su samu ba. Fatan mu duk masu niyyar Aure irin mu Allah Ya Mana jagoranci, Ya hore mana daga falalar Sa Ameen. Ya Allah ga bayin Ka suna son Ɗabbaka umarnin Manzon Ka (Sallallahu Alaihin Wasallam) Ya Allah, wanda ba Shi da kuɗin yin Aure Ya Allah Ka ba shi, irin mu kenan, wanda kuma yake da shi amma bai samu halin yi ba Ya Allah Ka ba shi Ikon yi. Ya Allah Ka sa mu Auri masu Taqwa da kwantar mana da hankalin mu a duk lokacin da muke cikin wani hali sannan su zama hanyar shigar mu Aljannah Ameen Ya Yayyu Ya Qayyum. WALLAHU A'ALAM Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. 𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G 𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇 Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇 https://t.me/TambayaDaAnsa ✍️𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏 𝐀𝐃𝐌𝐈𝐍 : 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟. +2348087788208
FALALA DA FA’IDAR YIN AURE: : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Assalamu alaiku Mal. Khamis Ina maka fatan Alkhairi 🙌🏽 Ubangiji Allah ya saka maka da Alkhairi irin kokari da kakeyi da jama'a, Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana mai Albarka.👏🏼 Mal. Khamis ina da tambaya ina so sanin falalar da fa'idan yin Aure Bisa Alkur'ani Da Sunnah.? : 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Walaikum sallam warahmatahi wabarkatahu; Aure yana da falala da alkhairai masu yawa a musulunci da kuma rayuwar ɗan adam ta yau da kullum. Shari'ar musulunci ta kwadaitar da yin aure domin yana kawo albarka, tsari, da kuma lada mai yawa ga ma'aurata waɗanda suka yi shi a matsayin Sunnar Ma'aiki (Sallallahu Alaihi Wa Sallam), kuma suka kiyaye dokokin shi. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kwaɗaitar da al'ummarsa akan suyi aure. Yace: "Ku auri Mafi soyuwa agareku cikin mata kuma masu haihuwa, domin dayawanku zanyi alfahari ranar alkiyama" kuma yace: "aure sunna-ta ne, duk wanda ba ya kwaɗayin sunnah-ta, to ba ya tare dani". An ruwaito Daga cikin manyan ɗaliban Abdullahi ɗan Abbas wato Abdullahi bn Jubairi Yace Abdullahi ɗan Abbas ya tambaye shi shin kayi aure? Sai yace bai yi ba, sai yace masa kayi aure domin mafi alherin wannan al'umma yana da aure. Wato yana nufin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) da manyan sahabbansa duk suna da aure don haka idan so kake kabi sunnar su to kayi aure. An karɓo hadisi daga Abdullahi ɗan Mas'ud (Allah Ya kara masa yarda), Manzon Allah (Sallallahu Alaihin Wasallam) Yace, ya ku taron matasa duk wanda ya samu iko daga cikin ku, toh yayi aure domin shi ne yafi taimakawa wajan rintse gani kuma shi ne yafi taimakawa wajan kare farji daga aikata zina, wanda bai samu iko ba toh na umarce shi da yin azumi domin azumi garkuwace gare shi. Bukhary da Muslim ne suka ruwaito shi. Bukhari 5065.Muslim 1400. Allah Ya faɗa a cikin Suratun Nisaa, inda Yace; ...فَانْكِحُوۡا مَا طَابَ لَـكُمۡ مِّنَ النِّسَآءِ مَثۡنٰى وَثُلٰثَ وَرُبٰعَ ۚ فَاِنۡ خِفۡتُمۡ اَلَّا تَعۡدِلُوۡا فَوَاحِدَةً اَوۡ مَا مَلَـكَتۡ اَيۡمَانُكُمۡ ؕ ذٰ لِكَ اَدۡنٰٓى اَلَّا تَعُوۡلُوۡا ؕ ...ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba. (Surah: An-Nisaa, Ayat: 3). وَمِنۡ اٰيٰتِهٖۤ اَنۡ خَلَقَ لَكُمۡ مِّنۡ اَنۡفُسِكُمۡ اَزۡوَاجًا لِّتَسۡكُنُوۡۤا اِلَيۡهَا وَجَعَلَ بَيۡنَكُمۡ مَّوَدَّةً وَّرَحۡمَةً ؕ اِنَّ فِىۡ ذٰ لِكَ لَاٰيٰتٍ لِّقَوۡمٍ يَّتَفَكَّرُوۡنَ "Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni. (Surah: Ar-Room, Ayat: 21). وَلَقَدۡ اَرۡسَلۡنَا رُسُلًا مِّنۡ قَبۡلِكَ وَ جَعَلۡنَا لَهُمۡ اَزۡوَاجًا وَّذُرِّيَّةً ؕ وَمَا كَانَ لِرَسُوۡلٍ اَنۡ يَّاۡتِىَ بِاٰيَةٍ اِلَّا بِاِذۡنِ اللّٰهِ ؕ لِكُلِّ اَجَلٍ كِتَابٌ "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika waɗansu manzanni, daga gabãninka, kuma Muka sanya mãtan aure a gare su da zũriyya, kuma ba ya kasancẽwa ga wani Manzo ya zo da wata ãyã, sai da iznin Allah. Ga kõwane ajali akwai littãfi. (Surah: Ar-Ra'd, Ayat: 38). Manzon Allah (Sallallahu Alaihin Wasallam) Yace; "Wanda yayi aure, hakika ya kammala rabin Addinin sa, toh ya ji tsoron Allah a sauran rabin" Watau ibadar da aka halicce ka don kayi ta, idan kayi aure, Allah Subhanahu Wa Ta'ala Ya ba ka rabin ta Ƙyauta. Manzon Allah (Sallallahu Alaihin Wasallam) Yace hakika idan ɗayan ku ya ga wata mãce sai ta kayatar da shi toh ya tafi wajan iyalin sa, hakika yin hakan zai mayar da abin da ya ji a zuciyar sa. Muslim ne ya ruwaito shi (hasanun sahihun). Daga Abdullahi ɗan Amr RA yace : Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: Duniya wani jin daɗi ce, amma mafi alherin jin daɗinta shine auren mace ta gari. Muslim 1467.
Idan miji yana neman matarsa ne kawai lokacin da yake bukata, hakan yana sa mace ta ji ana amfani da ita ne kawai, ba wai ana kaunarta ba. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya karfafa maza su kasance masu wasa da nishadantar da matansu, ba wai kawai su neme su lokacin biyan bukata ba. Ba laifi ba ne a shari'ar Musulunci mace ta ki yarda da bukatan mijinta na saduwa idan har yana wulakanta ta, baya kulawa da ita, kuma baya kyautata mata, musamman ma idan yana amfani da ita ne kawai lokacin da yake da bukata ba tare da bata hakkin rayuwa da kauna ba. Wajibi ne akan miji ya kyautata mata, ya ciyar da ita, da kuma bata kulawa ta gari akowane lokaci, ba kawai lokacin da yake son biyan bukata ba. Mijin da baya sauke hakkin matarsa na rayuwa ta gari zai iya sa matarsa ta ji babu dadi, kuma rashin ba shi hadin kai a irin wannan yanayi bai zama zunubi ba a gare ta, domin yana tauye mata nata hakkin. A muslunci, ba a son mutum ya yi mummunan addu'a ko tsinuwa ga kowa, har da wanda ya zalunce shi, domin addu'ar wanda aka zalunta a kan azzalumi karbabbiya ce. Yazo acikin hadisi cewa duk sanda wani yayi addu'a akan zaluncin da akayi masa, to Mala'iku sukan dauki wannan addu'ar akan giza-gizai, kuma Allah yakan ce masa "lallai sai na taimakeka koda bayan wani lokaci ne". Kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya gaya wa Sahabbai (Allah ya yarda dasu) cewa : "ku kiyayi addu'ar wanda aka zalunta. domin hakika babu wani abinda ke kangewa tsakaninta da Allah". Mafi alkhairi shi ne neman shiriyar Allah maimakon la'ana. Ki nemi lokaci mai kyau lokacin da kuke cikin natsuwa (ba lokacin da kuke fada ba). Ki fada masa yadda kike ji ta hanyar amfani da kalamai soyayya da girmamwa, ki Bayyana masa cewa kina son shi kuma kina son kusancinsa, amma rashin kulawar da yake baki yana kashe miki gwiwa. Idan kika gano cewa magana dashi kai-tsaye ba zata yi amfani ba ko kuma zai juyo miki da fada, zaki iya neman babban mutum da yake girmamawa a cikin danginsa ko naki don a zauna a fada masa gaskiya cikin hikima. Ki Kula Da Kanki Da Kwarin Gwiwarki, Kada kiyi kasa a gwiwa wurin kula da tsaftarki, kyawunki, da farin cikin zuciyarki. Wani lokaci canza dabi'unki da rashin damuwa da halayensa na iya sa ya fara tunanin me ke faruwa, har ya dawo yana neman kulawarki. Zaman aure yana bukatar hakuri da juriya, amma kuma yana bukatar mutunta juna da soyayya don rayuwar aurenku ta samu dorewa cikin farin ciki. WALLAHU A'ALAM Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. 𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G 𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇 Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇 https://t.me/TambayaDaAnsa ✍️𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏 𝐀𝐃𝐌𝐈𝐍 : 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟. +2348087788208 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
HUKUNCIN MIJIN DA MUSGUNA WA IYALINSA: : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Assalamu Alaikum mallam, shekarata goma sha hudu da aure da mijina amma baya kyautatamin kullum cikin fada da mita da kananun magana yake daga ni har yarana idan muka ganshi fargaba mukeji yasa mana tsoronshi arai, yana mana mulkin zalinci ba soyayya ba kulawa ba kyautatawa ko rashin lafiya nakeyi baya kula dani haka harzan warke baya zama damu idan yafita wani lokacin sai dare ko munyi bacci zaidawo, a haka a haka duk naji yafitamin arai, idan nayi kokarin samunshi muyi sulhu haka zai mayar da abun abun fada da tashin hankali a saidai yadauko abinda yawuce shekara da shekaru yayita fada, ahaka mallam sha'awan saduwa dashi duk yafitamin arai sbd duk abinda yakemin baida lokacina sai idan zai sadu dani ba magana mai dadi ba farinciki idan yagama kuma zaici gaba da rashin mutuncin dayakemin kamar ban taba masa rana ba sai kuma idan wani bukatar saduwan yakawoshi, mallam sbd haka duk saduwan auren yafitamin arai inata addua dai ba dare ba rana, mallam shin inada laifi idan nima naki yarda dashi lokacin dayazo saduwan saboda duk yaciremin sha'awanshi a raina, kuma da mallam ba haka nakeba ko rigarsa nagani sai hankalina yatashi bare idan naganshi da kudina nake biya group group nake shiga don nakoyi yadda ake gamsar da miji, kuma inayi shekara da shekaru amma duk yafitarmin arai saboda kuntatawa da rashin kyautatawa yasa ko shekara zanyi ba miji bazai dameni ba, mallam har hakan yasa ina mishi mummunar addua don dagani har yaranshi ba wanda yakejin dadinshi, don Allah atayani da addua kuma abani shawara sannan amin posting a group. Ni macece meson soyayya da kulawa amma dole haka na hakura bawai don banaso ba saidan bansamuba karfi da yaji yake nuna bazaiyiba inyi duk abinda zanyi, amma shi bazan samu daga wajenshi ba. : 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh. A addinin Musulunci, mijin da ke zaluntar iyalinsa, baya kula da su, kuma ya hana su hakkinsu na soyayya, tausayi, da kulawa, yana da laifi. Ya wajaba ya gyara halinsa, domin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce mafi alherin mutane shi ne wanda ya fi kyautata wa iyalinsa kuma ni ne mafi alherin ku ga iyalina. Mijin da ke kyautata wa matarsa da 'ya'yansa ta hanyar ciyarwa, da tausasawa, da sakin fuska yana samun babban lada kuma rayuwar aurensu tana dorewa cikin farin ciki. Allah ya haramta zalunci ga kansa da kuma tsakanin bayinsa. Mijin da ke cutar da matarsa ta hanyar duka, zagi, hana ta hakkinta na ciyarwa, ko kuntata mata yana da babban zunubi kuma zai fuskanci hukunci a duniya da lahira. Dole ne miji ya kula da matarsa idan tana rashin lafiya kuma ya bata magani ko abinci. Allah ya umarci maza da su zauna da matansu lafiya da kuma daidaito. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya umarci maza su kula da matansu su kuma kyautata musu. Bai halatta miji ya rika wulakanta matarsa, jifanta da miyagun kalamai, ko nuna mata halin ko-in-kula ba. Musulunci ya gina zaman aure a kan soyayya, jinkai, da kuma kyautata wa juna. Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kafin ya bar duniya, kafin Allah ya ɗauki rayuwarsa wasiyar da yake bayarwa ga Al'umman duniya masu Mata shi ne: "ku tausayawa Matayen ku, ku zauna da su cikin aminci da amana, ku kyautatawa rayuwar su kada ku kuntata musu" kuma Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yana cewa: "dukkanku masu kiwo ne. kuma za'a tambayi kowannenku dangane da kiwon da aka bashi". Sha'awar mace tana farawa ne daga yadda aka gina zuciyarta da soyayya ta gaskiya, yadda ake kyautata mata, da kuma yadda ake nuna mata ƙauna da kulawa a aikace da kalamai masu dadi, kafin a je ga saduwar gado. Idan babu magana ta gari kuma akwai cin mutunci, jiki ba zai taɓa bayar da haɗin kai ba. Mace tana bukatar kulawa da kalaman nuna kauna don ta ji tana sha'awar mijinta.